Kisa: Babu Dalilin Cigaba Da Zaman ‘Yan Arewa A Kudu – Mahdi Shehu

Sanannen ɗan kasuwar nan mazaunin garin Kaduna Dr Mahdi Shehu ya koka dangane da halin rashin tabbas da ‘yan Arewa ke shiga a yankin kudancin Najeriya, inda ya yi kira ga a gare su da suyi gaggawar dawowa gida Arewa.

Mahdi Shehu ya bayyana hakan ne a wata wasika da ya aike wa ‘yan Arewa mazauna kudanci, inda ya tunatar dasu baiwa da Allah ya yi wa yankin arewa na dukkanin abin da ɗan Adam ke bukata a rayuwa, bisa ga haka su dawo Arewa domin kaucewa halin rashin tabbas da suke fuskanta a kudancin.

“Jama’ar Kudu sun samu wurin zama a arewa ba tare da tsangwama ba, amma sakayyar da ake wa ‘yan Arewa a kudu ita ce kisa da tsangwama, lallai ba za a lamunci hakan ba”

Ɗan Kasuwar ya ƙara da cewar dukkanin sana’o’i da ‘yan Arewa ke gudanarwa a kudanci, an fi buƙatar wadannan sana’o’i a Arewa, sana’o’i irin su acaba da yankan farce da wankin huluna da gyaran takalma da sauransu.

Mahdi Shehu dai na mayar da martani ne biyo bayan ƙaruwar kisa da ake yi wa ‘yan Arewa a kudanci musanman yankin Inyamurai a kusan kullum.

Labarai Makamanta