Kimanin ‘Yan Najeriya 100 Cutar Lassa Ta Kashe A 2021 – NCDC

Rahoton dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a yayin da annobar korona ke ci gaba ratsa sassan Najeriya, sabon rahoton hukumar NCDC ya nuna cewa zazzaɓin Lassa ya halaka mutum 92 a shekarar 2021.

Kazalika, rahoton ya ce ya zuwa lokacin rahoton Mako na 50, jumillar mutum 454 ne suka harbu da zazzaɓin a ƙaramar hukuma 66 da ke jiha 16 na faɗin Najeriya da kuma Abuja babban birnin ƙasar.

Jiha uku daga ciki da suka haɗa da Edo (197) da Ondo (159) da Taraba (21) ne ke da kashi 83 cikin 100 na dukkan mutanen da aka tabbatar sun kamun.

Jihohin Bauchi da Ebonyi na da mutum 18 kowaccensu, a cewar NCDC.

Labarai Makamanta