Kimanin Shaguna 50 Gobara Ta Lamushe A Kasuwar Kurmi

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar kimanin shaguna 50 ne suka kone kurmus sakamakon gagarumar gobarar da ta tashi a fitacciyar kasuwar Kurmi ta jihara ranar Litinin.

Kasuwar Kurmi ta na daya daga cikin tsofaffin kasuwannin da ke birnin na Kano, cibiyar kasuwancin arewacin Najeriya shekaru aru-aru da suka gabata.

Iblitala’in wanda ya fara wurin karfe 2 na dare, ya shafi shagunan masu siyar da litattafai a kasuwar da sauran shaguna masu hada hadar kayayyakin bukatu.

Kamar yadda mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar, Alhaji Saminu Abdullahi yace, “Mun samu kiran gaggawa daga wani Malam Baba Nasidi wurin karfe daya da minti hamsin da takwas na dare kan cewa gobara ta tashi a kasuwar litattafai.

“Bayan samun bayanin, mun gaggauta aika masu kashe gobara zuwa wurin inda suka isa karfe biyu da minti bakwai domin kashe gobarar,” ya kara da cewa. Abdullahi ya ce shagunan kari guda 37 da aka yi na wucin-gadi tas suka cinye yayin da wasu shaguna hudu suka cinye bayan taimakon masu kashe wutar.

Ya kara da cewa, wutar ta tashi ne sakamakon wutar lantarki. Ya shawarci ‘yan kasuwan da sauran jama’a da su dinga kashe dukkanin makunnan kayan wutar su tare da kashe duk wani tushen wuta duk lokacin da ba a amfani da su.

Labarai Makamanta