Kimanin Mutum 2000 ‘Yan Bindiga Suka Sace Cikin Watanni Shida A Kaduna – Kwamishina

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce adadin mutane da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a jiyar sun kai 1,789 a cikin watanni shida, yayin da jami’an tsaro suka yi nasarar kashe ‘yan bindiga 161 tare da kame da dama daga cikin su cikin watannin.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gidan jihar Kaduna Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da rahoton tsaro, inda yace hare-haren ‘yan bindigar ya kashe fararen hula 285 a tsawon lokacin na watanni shidan yayin da batagarin suka kuma sace shanun da yawansu ya kai 1 da 133.

A cewarsa daga ranar 1 ga watan Yulin da ya gabata zuwa Satumba sai da ‘yan bindigar suka sace mutanen da yawansu ya kai 804 da kaso mai yawa a tsakiyar jihar inda aka saci mutane 508 a lokacin kadai.

Kwamishinan Ya ce an kama mutane 654 da ake zargi a tsawon lokacin da ake binciken.

Labarai Makamanta