Kimanin Mutane Dubu 300 Ne Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Raba Da Muhalli

An bayyana cewar sakamakon wata ƙididdiga da bincike da aka gudanar an gano kimanin mutane Dubu 300 ne bala’in rikicin manoma da makiyaya ya raba da muhallinsu a yankin Arewacin Najeriya, kuma ƙaruwar adadin alƙaluman na da tada tayar da hankali matuka.

Wata ƙungiyar bincike mai zaman kanta a tarayyar Najeriya Zinariya Consult ta fitar da sakamakon inda ta ƙiyasta cewa sama da mutum dubu 300 sun rasa muhallansu a jihohi 4 na ƙasar sakamakon rikicin manoma da makiyaya a faɗin Najeriya.

Jaridar DailyTrust ta rawaito cewa ɗaya daga cikin jagororin binciken, Dr Joseph Ochogwu, ne ya shaida hakan a wani taron tattaunawa da manema labarai.

A cewar Ochogwu in ji jaridar, jihohin da ke fuskantar ƙaruwar irin wannan rikici sun hada da Benue da Plateau da Nasarawa da Taraba da Adamawa da Kaduna.

Wannan yanayi da ake ciki ya haifar da rasa rayuka da asarar dukiyoyi da raba dubbai da muhallansu.

Rikicin manoma da makiyaya rikici ne wanda ya daɗe yana ci wa jama’a tuwo a ƙwarya musanman a yankin Arewacin Najeriya, inda ke haifar da asarar tarin dukiyoyi da rayuka a kusan kowace shekara.

Daga bisani rikicin ya sauya salo inda ya koma ta’addancin ‘yan Bindiga, sakamakon yadda Fulani makiyaya da dama suka sauya tsarin nasu zuwa ayyukan kisa da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa a sassa daban daban na kasar.

Jihohi irin su Katsina Zamfara da Kaduna sune akan gaba wajen fuskantar wannan ta’asar, lamarin da yaja hankalin Gwamnati ta tarayya da Jihohi akan hanyoyin da za a bi wajen shawo kan rikicin.

Labarai Makamanta