Wani rahoto da wata cibiyar tattara bayanan sirri ta SB Morgen Intelligence ta wallafa ta ce an kashe jami’an tsaro a Najeriya da suka kai 966 a shekara guda.
Cibiyar ta saki rahoton ne a ranar Alhamis, bayan tattara bayanan sirrin da ta yi na hare-hare da aka kai wa jami’an tsaro daga watan Oktoban 2020 zuwa Satumbar 2021.
Rahoton ya bayyana ma’anar yaƙi a matsayin duk wani rikici da aka kashe mutum aƙalla 1,000. “Saboda wannan za mu iya cewa Najeriya na cikin yaƙi,” a cewar rahoton.
Zuwa yanzu babu wani martani daga hukumomin tsaron Najeriya game da rahoto.
You must log in to post a comment.