Ketare: Za A Gudanar Da Sallar Rokon Ruwa A Saudiyya

Labarin dake shigo mana daga Riyadh babban birnin ƙasar Saudiyya na bayyana cewar Sarki Salman na kasar ya buƙaci a gudanar da addu’o’in roƙon ruwa a ranar Litinin.

A sanarwar da ya fitar, ya buƙaci kowa ya tuba ya koma ga Allah da kuma ci gaba da gudanar da ayyukan alkhairi kamar su taimakon jama’a da bayar da sadaka da addu’o’i inda ya ce duka waɗannan sunnoni ne masu ƙarfi.

Ma’aikatar harkokin addini ta ƙasar ta sanar da daidai lokacin da za a yi addu’o’in inda ta ce minti 15 bayan fitowar rana a duka yankunan ƙasar.

Labarai Makamanta