Ketare: Za A Gudanar Da Kuri’ar Raba Gardama Kan Shan Sigari A Switzerland

Masu kada kuri’a a Switzerland za su yi zaben raba gardama don yanke shawara kan tsaurara dokokin ta’ammali da tallan taba sigari, musaman a duk inda matasa za su iya ganinta.

Ƙasar wacce kusan kashi ɗaya bisa huɗu na al’ummarta ke shan sigari, na da dokokin da ake ganin sun yi sauki, ga tallanta.

Masu fafutuka a Switzalan na ta jan kafa wajen ganin an tabbatar da gyara a dokar, wani abu da ake dangantawa da siyan bakinsu da kamfanonin samar da taba sigarin na yi.

Kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta baya-bayan nan dai na nuni da cewa galibin masu kada kuri’a na son a amince da shirin.

Masu kada kuri’a a Switzerland za su yi zaben raba gardama yau Lahadi don yanke shawara kan tsaurara dokokin ta’ammali da tallan taba sigari, musaman a duk inda matasa za su iya ganinta.

Labarai Makamanta