Ketare: Wasu Da Suka Karbi Rigakafin Korona Sun Mutu

Hukumomi a kasar Denmark dake nahiyar Turai a ranar Alhamsi sun dakatar da yiwa mutane rigakafi korona na tsawon makonni biyu bayan wata mata wacce aka yiwa ta samu taruwar jini kuma ta mutu nan take.

An dauki “wannan mataki ne bayan jini ya taru a jikin wasu mutane da aka yiwa rigakafin Kornanan Astrazeneca,” kamar y hukumar lafiyan Denmark tace a wani jawabi.

“Bamu tabbatar ba tukun ko akwai alaka tsakanin rigakafin da kuma taruwar jinin.” Hakazalika, kasar Norway ta dakatad da amfani da rigakafin Astrazeneca.

Gabanin haka kasar Austria ta sanar da cewa ta dakatar da amfani da rigakafin bayan watan malamar jinya yar shekara 49 ta samu matsalar taruwar jini yan kwanaki da yin rigakafin.

Bayan haka Kasashen Turai hudu – Estonia, Latvia, Lithuania da Luxembourg – sun bi sahu inda suka dakatar da yin rigakafin ba tare da ɓata lokaci ba.

Najeriya ta ƙaddamar da fara rigakafin Astrazeneca na Korona a ranar Juma’a. Sannan a ranar Asabar aka tsirawa shugaban ƙasa da mataimakinsa rigakafin kuma annuna a kafar talabijin kai tsaye.

Gwamnatin tarayya ta ce allurar rigakafin da za’a yiwa ‘yan Najeriya iri ɗaya ce da wanda akayima shugaban ƙasa Muhammadu Buhari. Shugaban hukumar lafiya, Dr. Faisal Shu’aib ne ya faɗi hakan yayin taron kwamitin yaƙi da cutar corona a Abuja.

Labarai Makamanta