Ketare: Malawi Ta Nada Mike Tyson Jakadan Wiwi

Ministan noma a Malawi ya rubutawa tsohon dan wasan dambe Mike Tyson takardar ba shi mukamin jakadan fannin noman Wiwi na kasar.

Lobin Lowe ya ce halatta noman tabar wiwi da gwamnati ta yi a shekarar da ta gabata, ya bude wata dama ta samun aikin yi a ciki da wajen Malami.

Ma’aikatar aikin noma a kasar ta ce, hukumar da ke kula da noman wiwi ta Amirka ta fara tuntubar Tyson kan batun.

Mista Lowew ya rubuta cewa; ”Ta yiwu Malawi ba za ta iya aikin ita kadai ba, sakamakon yadda kasuwancin ke bukatar hadin gwiwa. Don haka ina farin cikin nada ka Mista Mike Tyson a matsayin jakadan sanbfurin tabar wiwi ‘yar Malami.”

Tyson dai dan kasuwa ne da ya zuba jari a harkar noman wiwi. Kafar yada labaran Malawi ta rawaito cewa a mako da ya wuce aka sa rai Tyson zai je Malawi, to amma an dage zuwan sai nan gaba.

Labarai Makamanta