Ƙungiyar haɓaka tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma, Ecowas, ta yi wadarai da juyin mulkin da sojoji suka yi a Burkina Faso, tana mai bayyana shi da “koma-baya” bayan ci gaban da aka samu.
“Ecowas na jaddada rashin amincewarta da ƙwace mulki ba ta hanyar da kundin tsarin mulki ya tanada ba,” a cewar sanarwar da ta fitar.
Ta ƙara da cewa “muna kira da a yi gaggawar komawa kan yarjejeniyar da aka cimma ta mayar da mulki ga farar hula a ranar 1 ga watan Yulin 2024”.
Ƙungiyar mai hedikwata a Abuja ta gargaɗi “duk wani mutum ko tawaga waɗanda aikinsu zai iya kawo tsaiko wajen mayar da mulki ga farar hula ko kuma tayar da hankali a Burkina Faso”.
Ita ma takwararta ta AU ta yi Allah-wadai da juyin mulkin, wanda Kaftin Ibrahim Traore ya jagoranta inda ya hamɓarar da Kanar Damiba wanda ya hau mulki a watan Janairun da ya wuce ta hanyar juyin mulki.
You must log in to post a comment.