Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Ketare: An Yi Yunkurin Kifar Da Gwamnatin Sudan

Wasu rahotanni da ke fitowa daga Sudan na cewa an yi yunkurin juyin mulki a kasar.

Rahotanni sun ce wasu sojoji da ba a tantance ko su waye ba sun yi wa gidan firaminista Abdallah Mandok kawanya.

Rahotanni na cewa dakarun kasar sun cafke ‘yan majalisar ministocin gwamnatin hudu, da kuma farar hula daya mamba a cikin gwamnatin hadaka.

Har wa yau, an bada rahoton cafke mai bai wa mista Hamdok shawara kan harkokin yada labarai.

Kungiyar kwararru a Sudan sun yi kira ga jama’a da su fito kan tituna domin nuna bijirewa juyin mulki.

A ranar Alhamis, dubban ‘yan kasar suka cika titunan birnin Khartoum domin nuna goyon baya ga gwamnatin rikon kwarya.

Dakarun Sudan da kuma shugabannin fararen hula a kasar ba sa ga maciji da juna.

Dukkan bangaroirin biyu na cikin gwamnatin hadaka tun shekarar 2019, abin da ke nuna cewa suna share fagen gudanar da zabuka a kasar.

A ranar Alhamis, dubban mutane sun yi zanga zanga a sassan kasar domin nuna goyon baya ga mulkin dimokradiyya.

Exit mobile version