Ketare: An Soki Saudiyya Kan Sayen Kungiyar Kwallon Kafa

Rahotanni daga Kasar Saudiyya na bayyana cewar Karɓe ragamar ikon ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Newcastle da wani kamfanin Saudiyya ya yi a Ingila ya faranta wa mutane da dama amma kuma masu suka da yawa sun yi Allah-wadai da matakin.

Ga wasu dalili shida da suka sa lamarin ya jawo wa babbar ƙasa mai tsarki suka.

Gawurtaccen kisan gilla

Kimar Saudiyya ta yi matuƙar faɗuwa game da kisan Jamal Khashoggi a 2018, wani shahararren ɗan jarida mazaunin Amurka wanda ya sha sukar gwamnatin ƙasar.

Wani lauya mai kare haƙƙin ɗan Adam da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ɗauka aiki ya ce wasu ma’aikatan Saudiyya “sun yi gunduwa gunduwa Khashoggi cikin rashin tausayi” a ofishin jakadancin ƙasar na birnin Istambul da ke Turkiyya.

Rahoton ya alaƙanta Yarima Mai Jiran Gado Mohammed bn Salman da kisan da kuma wasu manyan shugabannin ƙasar. Duk da cewa Yariman ya musanta hannu a kisan, kimarsa ta yi matuƙar zubewa a ƙasashen duniya.

Budurwar Jamal Khashoggi, Hatice Cengiz, ta siffanta sayen Newcastle da Saudiyya ta yi a matsayin “abin ɓacin rai”.

Mohammed bin Salman ne shugaban gidauniyar Saudiyya wadda ta mallaki kashi 80 cikin 100 na hannun jarin Newcastle, duk da cewa hukumomin Premier League sun ce an ba su tabbacin cewa kulob ɗin ba zai kasance ƙarƙashin gwamnatin Saudiyya.

A 2018, hukumomin Saudiyya sun tsare mata 13 masu fafutikar kare haƙƙi da suka jagoranci kamfe na neman cire haramcin tuƙin mota kan mata.

An yi zargin cewa an azabtar da huɗu daga cikinsu sannan masu binciken sun ci zarafinsu.

A 2020, wata kotun musamman kan ta’addanci ta samu wadda ta fi shahara a cikin matan mai suna Loujain al-Hathloul da laifi.

Ta musanta zarge-zargen kuma masu kare haƙƙi na Majalisar Ɗinkin Duniya sun bayyana su da “na ƙarya”.

Labarai Makamanta