Ketare: Adadin Wadanda Suka Mutu A Turmutsitsin Koriya Sun Doshi 200

Mutum aƙalla 154 ne suka mutu ranar Asabar a birnin Seoul na Koriya ta Kudu sakamakon turereniyar da ta faru a bikin Halloween, a cewar ‘yan sandan birnin.

Cikin mutanen da suka mutu, 98 mata ne da kuma maza 56.

‘Yan sanda sun tantance 153 daga cikinsu kuma sun sanar da iyalansu, kamar yadda rahoton kamfanin labarai na Yonhap ya ruwaito.

Ana ci gaba da tantance mamaci ɗaya, yayin da wasu 133 suka ji raunuka, a cewar hukumar kashe gobara.

Labarai Makamanta