Kebbi: ‘Yan Bindiga Sun Harbe DPO Da ‘Yan Sanda Takwas

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani DPO da jami’ansa takwas a Jihar Kebbi da ke arewacin kasar.

Kakakin yan sandan na Jihar Kebbi ASP Nafi’u Abubakar ne ya tabbatarwa BBC da faruwar lamarin, wanda ya faru a ranar Lahadi.

“Da misalin karfe 2:30 na rana ne DPO na Kasaba ya samu labarin an kai hari wani kauye da ake kira Makuku da wasu kauyuka da ke kewaye da shi, nan da nan ya debi yaransa su takwas da nufin kai dauki bayan fafatawa kuma anan suka gamu da ajalinsu,” in ji ASP Nafi’u.

Rahotanni sun ce Sanata mai wakiltar yankin Bala ibn Na’alla ya nemi taimaon rundunar sojin sama, inda nan da nan jirgin yaki ya kawo dauki tare da fatattakar ‘yan bindigar, sai dai babu rahoton kashe kowa cikinsu.

Ko a ranar Talatar da ta gabata Sai da ‘yan bindigar suka farwa kauyukan Kunduru da Bajida da Rafin Gora inda suka yi awan gaba da shanu da dama.

A yanzu haka mutanen kauyukan sun fara barin muhallansu domin tsira da rayukansu.

Labarai Makamanta