Kebbi: Hatsarin Kwale-Kwale Ya Ci Rayukan Mutane 10

Ana cigaba a aikin nemo gawar mutane 10 da suka nutse a hatsarin jingir ruwan fasinjoji daya auku a Tungar Gehuru dake Karamar Hukumar Jega Jihar Kebbi.

Tuni shugaban Karamar Hukumar Mulki Ta Jega Hon Barr Shehu Marshal wanda Alh Adamu Isiya Kimba ya wakilta da Kuma shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Jihar Kebbi Alh Sani Dododo da tawagar su suka isa yankin.

Jirgin yana dauke da fasinjoji 10 inda 8 suka hallaka, an samu nasarar ceto biyu a raye. Zuwa yanzu da muke hada wannan rahoto an tsamo gawar mutum 4 ana cigaba da aikin neman 4 da har yanzu ba’a gan suba.

A zantawar mu da matukin jirgin Abubakar Sani ya bayyana alhinin sa matuka bisa aukuwar wannan hatsari.

Daga karshe Alh Sani Dododo shugaban hukumar bada agajin gaggawa ya bayyans irin yadda gwaunati ke cike da damuwa bisa aukuwa wannan hatsari tare da gabatar da sakon jajantawa ga daukakin al’ummar yanki.

Allah yaji kan musulmin da suka rigamu. Idan tamu tazo Allah ya bamu cikawa da imani.

Labarai Makamanta