Kebbi: An Shiga Cece-Kuce Tsakanin INEC Da PRP

Rahotanni daga Jihar Kebbi na bayyana cewar a yayin da ake shirye-shiryen zabukan kananan hukumomi a jihar ana ka-ce-na-ce tsakanin jam’iyyar adawa ta PRP da kuma hukumar zaben jihar.

Rikicin ya biyo bayan da hukumar ta ki saka jam’iyyar a cikin wadanda za su fafata a zaben kananan hukumomi wanda za a yi a karshen makon nan.

INEC ta bayyana cewar ta ɗauki matakin ne bayan da jam’iyyar PRP gaza biyan kudaden da hukumar ta bukaci ‘yan takara su biya.

Sai dai anata ɓangaren Jam’iyyar PRP tace ta ki biyan wadannan kudade ne bisa hujjar cewa babu tanadin biyan kudin a kundi tsarin mulki har ma ta maka INEC a kotu.

Labarai Makamanta