Kayyade Kudaden Kananan Hukumomi: Gwamnoni Za Su Garzaya Kotu

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar gwamnoni ta ce za ta ɗaukaka ƙara game da hukuncin wata babbar kotu da ya kori ƙarar da suka shiga suna ƙalubalantar matakin da sashen tattara bayanan sirri kan hada-hadar kuɗi na ƙayyade kuɗaɗen da ƙananan hukumomi za su rika kashewa a kullum.

A hukuncin da babbar kotun ta yanke ta ce gwamnonin ba su da hurumin hana kayyade naira dubu 500,000 a matsayin kuɗaɗen da ƙananan hukumomi za su rika kashewa a kullum ba.

Abdulrazak Bello Barkindo daraktan yaɗa labarai na ƙungiyar ya ce duk da cewa taron da gwamnonin suka shirya ranar Laraba bai yiwu ba, amma an cimma matsayar ɗaukaka ƙara kan hukuncin babbar kotun.

Labarai Makamanta