Kawar Da Zakzaky Da Gardawansa Nasara Ce Ga Rundunar Soji – El Rufa’i

An yaba gami da jinjinawa rundunar sojin Najeriya ƙarƙashin jagorancin shugaban dakarun rundunar na kawar ‘yan ta’adda da ta’addanci a tarayyar Najeriya musamman yankin Arewacin Najeriya.

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El Rufa’i ne ya yi wannan yabon lokacin da yake jawabi a matsayin shi na mai masaukin baƙi a babban taron rundunar sojin Najeriya da ke gudana a Kaduna a yau din nan.

El Rufa’i ya cigaba da cewar, bai yiyuwa ayi magana akan nasarar rundunar sojin Najeriya ba tare da an ambato kokarin da rundunar ta yi na kawar cutarwar da Zakzaky da gardawansa suka rinƙa yi a jihar Kaduna musamman birnin Zazzau na tsawon shekaru sama da 30 ba, wanda ayau jama’ar jihar Kaduna na zaune lafiya.

A jawabin mai girma shugaban ƙasa Buhari ya nuna gamsuwa da ƙoƙarin da rundunar soji keyi na yakar ta’addanci musamman a yankin Arewa maso Gabas, wanda babu mai shakkar cewa an samu tsaro a Najeriya a zamanin mulkin mu idan aka kwatanta da halin da kasar take ciki a baya.

Shugaban ya kuma mika sakon ta’aziyar shi ga iyalan sojoji wadanda suka rasa rayukansu a yayin yaƙi da Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ta’addanci inda ya yi musu addu’ar fatan samun rahamar Ubangiji.

Related posts