Kawar Da CORONA A Najeriya: Buhari Zai Ciwo Bashin Triliyan 3.2

Ministar Harkokin Kudade Zainab Ahmed ce ta bayyana haka, ranar Litinin a Abuja, lokacin da ta ke bude asusun neman lamunin naira bilyan 500 da za a fara fafata yaki da cutar Coronavirus kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Ta ce Najeriya ta fara tsara yadda za a ciwo bashin har na naira tiriliyan 3.2 domin gagarimin aikin kakkabe cutar Coronavirus a kasar nan.

Zainab ta bayyana yadda za a ciwo bashin, inda ta ce mafi yawan kudaden za su fito ne daga Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF), Bankin Duniya da kuma Bankin Bunkasa Kasashen Afrika.

“Za mu karbo bashin dala bilyan 7.05(kwatankwacin naira tiriliyan 2.68) a kan farashin kowace dala kan naira 380.

“Wadannan kudaden za a yi amfani da su wajen Inganta wannan shirin yaki da Coronavirus na naira bilyan 500.

“Tuni har mun cika fam na neman a ba mu bashin gaggawa na naira dals bilyan 3.4 daga Bankin Bada Lamunina Duniya domin mu yi wa Coronavirus kwaf-daya da kudaden.

Related posts