Kauyawa Sun Fi Kowa Shiga Wahala Kan Sauya Takardun Naira – El-Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bukaci babban bankin Najeriya (CBN) da ya tsawaita wa’adin daina karbar tsoffin takardun kudi cewa lokacin ya yi gajarta da yawa, kuma jama’a na shan wahala sosai.

Babban bankin Najeriya dai ya ce za a daina amfani da tsoffin kudade a kasar daga ranar 31 ga watan Janairu lamarin da ya jefa al’umma musamman talakawa a halin wayyo Allah.

El-Rufai ya bayyana cewa mutanen karkara da dama wadanda basu da hanyar yin hada-hada kudi sune wadanda wannan hukunci zai fi shafa.

Da yake jawabi a wata hira da manema labarai a karamar hukumar Kubau ta jihar Kaduna, gwamnan ya nanata cewa babu ta yadda za a yi manoman karkara da yan kasuwa a yawancin garuruwan jihar su cika wa’adin CBN na kai tsoffin kudinsu banki.

Ya bayyana cewa wasu kananan hukumomin basu da kowane banki a cikinsu, don haka ba a sako su cikin wannan tsari ba kenan.

Labarai Makamanta