Katsina: ‘Yan Sanda Sun Tarwatsa Shirin ‘Yan Bindiga

Labarin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar Gwarazan yan sanda sun dakile harin yan bindiga, waɗan da suka farmaki ƙauyen Faɗimawa a karamar hukumar Kurfi dake jihar.

Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Kastina, Gambo Isa, ya tabbatar da haka ranar Jumu’a, a ganawarsa da manema labarai a birnin Katsina.

Mazauna ƙauyen sun bayyana cewa yan ta’addan sun shiga da sanyin safiyar ranar Alhamis, kuma suka sace adadi mai yawa na dabbobin jama’a, Da aka sanar da yan sandan Kurfi, nan take suka kai ɗauki ƙauyen, suka yi musayar wuta da maharan, a wannan lokaci ne suka kwato baki ɗaya dabbobin da suka sace.

Da yake tabbatar da lamarin, kakakin yan sandan jihar ya ce: “A ranar 27 ga watan Janairu, wasu yan ta’adda suka farmaki kauyen Faɗimawa dake ƙaramar hukumar Kurfi, inda suka sace dabbobi masu yawan gaske.” “Shugaban ofishin yan sanda na Kurfi ya jagoranci tawagar yan sanda zuwa ƙauyen, kuma suka tari yan ta’addan akai batakashi.”

“Dabaru da jajircewar yan sandan ta sa suka fi ƙarfin yan ta’addan kuma suka kwato dabbobin da suka sace. Mafi yawan yan ta’addan sun gudu da raunin bindiga.” Ya ƙara da cewa tuni jami’ai suka bazama cikin dazukan dake kusa da nufin kamo yan bindigan ko gano gawarwakin su.

Labarai Makamanta