Katsina: ‘Yan Sanda Sun Kwato Rokoki Da Manyan Bindigogi Hannun ‘Yan Bindiga

Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Gambo Isah ya bayyana cewa dakarun ‘yan sanda a jihar sun kwato manyan makamai daga hannun ‘yan bindiga a jihar a cikin shekara 2021.

Isah ya ce baya ga makamai an damke yan iska, batagari da ‘yan takife sama da 900 a tsawon wannan shekara.

” Manyan Bindigogi kirar GPMG 4, AK-47 44, bindiga LAR rifle guda daya, G3 guda daya, bindigogi 20 kirar adaka, harsasai masu girman milimita 7.62 na daga cikin makaman da ‘yan sandan suka kama.

Isa ya ce rundunar ta ceto dabobbi 1,243 da barayi suka sace. A ciki akwai shanu 867, tumakai 352, akuya 24 da jaki daya.

“Jami’an tsaron sun Kuma kama ‘yan fashi da makami, barayin dabobbi da dai sauran su.

“An kama masu garkuwa da mutane 157 inda daga ciki an kai mutum 145 kotu sannan ana yin bincike akan sauran mutum 12.

“An kama masu garkuwa da mutane mutum 65 inda a ciki an kai mutum 63 kotu ana yin bincike akan mutum biyu.

“An kama barayin dabbobi mutum 244 an kai mutum 230 daga cikinsu kotu sannan ana kan gudanar da bincike akan mutum 14.

“Jami’an tsaron sun kashe ‘yan bindiga 38 sannan ‘yan sanda biyar sun mutu.

“An kama mutum 246 da laifin fyade da wasu laiffuka, an ceto mutum 63 daga hannun masu safaran mutanen Wanda aika aika wa ofishin hukumar NAPTIP dake jihar Kano.

Labarai Makamanta