Katsina: ‘Yan Sanda Sun Hallaka ‘Yan Bindiga Masu Yawa

Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar Rundunar ‘yan sanda ta yi nasarar aikewa da wasu tulin ‘yan bindiga lahira, sannan ta samu nasarar cafke wasu 16 tare da kwato shanun da suka sace a jihar.

Yan sandan sun kuma kwato wani adadi na miyagun ƙwayoyi daga hannun yan bindigan. Kakakin hukumar yan sanda na jihar Katsina, SP Gambo Isa, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ranar Laraba.

Isah yace an kama yan bindigan ne lokacin da sukayi artabu tsakanin yan sanda da yan bindigan a wasu daga cikin ƙananan hukumomin jihar. Isah yace: “Jami’an yan sanda sun kashe yan bindiga biyar lokacin da suka yi musayar wuta a ƙananan hukumomin Kafur, Ɗanja, Ɗutsin-ma, Safana, Batsari da kuma Maƙera a Funtua.”

“Jami’an sun kuma samu nasarar cafke wasu guda 15 a fafatawar da suka yi, Yayin da suka damƙe wani mai suna Musa Shamsuddin, da zargin yana zuwa cikin jeji duba lafiyar yan bindigan da suka ji rauni.” “An ƙwato bindigogi da kuma wani adadi na alburusai masu yawa a hannun yan bindigan.

Labarai Makamanta