Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Yi Ta’adi A Ƙaramar Hukumar Sabuwa

A cikin daren Jiya Litinin “yan ta’adda sun shiga unguwar Bako, Kwarawa, Arewaci a gundumar Mai Bakko dake cikin karamar hukumar Sabuwa a jihar Katsina, inda suka ci karensu babu babbaka har suka fice.

Wakilin mu ya shaida mana cewa kashe mutane sama da goma, sun yi awon gaba da mutane sama da 30 tare da balle shagunan jama’a da raunata mutanen da ba’asan adadinsu ba har yanzu.

A cikin ‘yan kwanakin nan Yan ta’adda sun addabi al’ummar karamar hukumar Sabuwa duk da cewa akwai matsugunnin sojoji a yankin, amma a haka ‘yan ta’adda suke shigowa suci karensu ba babbaka, wanda a kullun sai sun shigo sun kashe mutane sun kwashi dabbobi da balle shagunan jama’a tare garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Muna Kira ga Gwamnati da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki da su tausayawa al’ummar wannan yaki su gaggauta kawo masu dauki da sauran garuruwan dake fama da matsalar tsaro a wadannan yankuna, domin a kullun suna cikin fargaba basu iya barci a gidajensu.

Allah Ya kawo mana karshen wannan masifa a yankinmu da Arewa da Najeriya baki daya.

Labarai Makamanta