Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Yi Gaba Da Surukar Sanata

Labarin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewa wasu gungun ‘yan bindiga sun yi awon gaba da mutum hudu cikin su har da surukar Sanata mai wakiltar mazaɓar Katsina ta arewa a majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Babba Kaita.

Wani mazaunin garin Kankia, Malam Muhammad Sani, ya ce maharan sun farmaki garin ne a farkon awannin ranar Litinin kuma suka ci karen su babu babbaka na tsawon awanni.

Ya ce faramakin ya faru ne a Anguwar Bakin Kasuwa, inda yan bindigan suka kutsa kai gidan Mani Babba Kaita, ƙanin Sanata Ahmed Babba Kaita, suka yi awon gaba da matarsa.

Ya ƙara da cewa maharan sun kuma shiga gidan wani Sabe Halilu a wannan Anguwa, inda suka ci zarafin matarsa kana suka sace ƴaƴansa biyu, cikin su har da ɗalibar Firamare.

Wani mazaunin Kankia na daban, Salisu Musa, ya ce maharan sun sace wata matar aure duk a wannan Anguwa ta Bakin Kasuwa. Mutumin ya ce: “Gaskiya sun zo ne da nufin sace ɗan uwan Sanatan, amma ya fice daga gidan.

Ɗaya daga cikin matansa ta tsira, amma wacce abun ya shafa ta ga ba zata iya guduwa ta bar ƴaƴanta ba, shiyasa suka same ta.”

“Ɗayar matar kuma mijinta baya nan lokacin da suka zo, yayin da ta yi nufin guduwa sai maharan sun cafko ta suka lakaɗa mata duka, suka haɗa da ‘ya’ya biyu. A baki ɗaya harin, sun sace matan aure biyu da kananan yara biyu.”

Labarai Makamanta