Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mata Masu Yawa

‘A daren ranar Litinin ne, ‘yan bindiga dauke da manyan bindigogi suka kai hari a kauyen Katsalle da ke cikin karamar hukumar Sabuwa a jihar Katsina, inda suka sace Mata talatin suka tsallaka da su daji.

Wani mazaunin garin na Katsalle ya shaida mana ta waya cewa ‘yan bindigar sun zo garin na Katsalle da misalin karfe sha biyu na daren jiya, akalla sun kai arba’in bisa mashina dauke da bindigogi kowanen su. Da muka ga tahowar su day makamai sai muka labe, mun yi yunkurin kaiwa matan dauki amma abun ya gagara, saboda muna jin kukan su day na Yara suna neman taimako, ba yadda za mu yi, akwai gidan da suka dauki mace goma.

A shekaran jiya, sun kai hari a kauyukan Unguwar Tukur da Sabon Layin Mai Keke, inda Unguwar Tukur sun dauki Mata goma, sai kuma Sabon Layin Mai Keke sun arce da Mata goma sha biyar a daren shekaran jiya Lahadi.

Duk yunkurin da wakilinmu ya yi na jin ta bakin kakakin rundunar’yan sanda na jihar Katsina, SP Gambo Isa ya ci tura har zuwa aiko da wannan rohotan, saboda an buga wayarsa tana karaurawa amma ba’a dauka. Amma an jiyo kakakin a wata kafa ta kasashen waje yana cewa suna jiran rohatan baturen yan sanda na karamar hukumar Sabuwa.

Labarai Makamanta