Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Sake Sace Tarin Jama’a A Faskari

Bayan sace ‘yan makarantar sakandire ta Kimiyya ta garin Kankara, sama da dari uku da talatin da ukku, a ranar juma’a da ta gabata. ‘Yanbindiga dauke da makamai sun kai hari a Kauyen Jar Kuka da ke da tsawon kilomita goma da karamar hukumar Faskari a jihar Katsina,inda suka sace maza goma sha ukku da Mata hudu a daren jiya Talata.

Majiyarmu ta shaida mana cewa ‘yan bindigar sun zo ne a kasa, inda suka fara harbe-harbe a sama, anan take suka tafi da mutane goma sha bakwai da dabbobi da mashinan hawa guda hudu na mutanen garin.

Karamar hukumar Faskari, na cikin kananan hukumomi da ke fama da matsalar tsaro a jihar Katsina kuma nan ne helkwatar rundunar sojoji masu yaki da yan bindiga na musamman da aka yi wa lakabi da (Operation Sahel Sanity).

Jihar Katsina na cikin Jihohin da ke yankin Arewa maso yamma inda Fitinar ‘yan Bindiga ke ƙara ruruwa, a ƙarshen makon da ya gabata ne ma ayarin wasu ‘yan Bindiga suka dira makarantar kimiyya da ke karamar hukumar Ƙanƙara inda suka yi awon gaba da ɗaruruwan ɗalibai.

Labarai Makamanta

Leave a Reply