Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Sake Sace Ɗalibai

Rahotannin dake shigo mana yanzu daga Jihar Katsina na bayyana cewar wasu ‘yan Bindiga ɗauke da manyan makamai sun sace wasu dalibai dake Makaranta Sakandaren kauyen Gobirawa da ke karamar hukumar Safana a jihar Katsina a ranar Talata.

Wani mazaunin kauyen Gobirawa wanda ya nemi a boye sunansa, ya tabbatarwa Daily Trust cewa an sace daliban ne bayan an tashe su daga makaranta a Community Day Secondary School a Gobirawa.

“Ba makarantar kwana bace kuma dukkan daliban uku da aka sace maza ne kuma suna hanyar komawa gidansu ne da rana bayan an tashi makarana,” a cewar majiyar.

Majiyar ta kara da cewa ana ganin kamar cewa gwamnatin jihar ta bada umurnin rufe makarantar bayan afkuwar lamarin.

An yi kokarin ji ta bakin jami’an makarantar amma hakan bai yiwu ba domin kwamishinan Ilimi na jihar, Dr Lawal Badamasi bai amsa kirar da aka masa a waya ba.

Shi kuma mai magana da yawun ma’aikatar ilimin jihar Katsina, Sani Danjuma ya ce bai da labarin afkuwar lamarin domin baya jihar ya yi balaguro domin yin wani aiki.

Da aka tuntube shi, kakakin ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce zai kira ofishin DPO na karamar hukumar Safana domin tabbatar da sahihancin rahoton.

Labarai Makamanta