Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban APC

Wasu ƴan bindiga sun sace shugaban jam’iyyar APC na mazaɓar Ɗantankari A da ke ƙaramar hukumar Ɗandume a jihar Katsina.

Mazauna garin sun ce an sace shugaban jam’iyyar ne tare da wata mata da ɗan kishiyarta.

Ƴan bindigar sun shiga garin ne da daren ranar Alhamis suka sace shugaban jam’iyyar Alhaji Shafiu Ɗantankari da sauran mutanen biyu.

Har ya zuwa lokacin haɗa wannan labari, rundunar ƴan sandan jihar Katsina bata ce komai ba a kan batun ba.

Labarai Makamanta