Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 20

Da yammacin jiya Laraba ne, ‘yan bindiga dauke da manyan bindigogi suka kai harin a kauyukan Maradi da Fan Dogari da Damawa da Cikawa da Suda da Gayuna da ke gundumar Wurma a karamar hukumar Kurfi ta jihar Katsina, inda suka kashe sama da mutane ashirin har lahira tare da kona gidaje da dama a garuruwa.

Majiyarmu ta shaida mata cewa ‘yan bindigar sun shigo wadannan garuruwa masu makwabtaka da juna da marece jiya Talata, bisa babura da bindigogi, sama da dari, inda suka fara harbe-harbe kan mai uwa-da-wabi, duk inda suka je wuta suke sanya wa garin, duk ya ruga su halbe shi, kuma kowane gari da na lissafo haka suka yi.

Don gaskiya mutanen da suka kashe sun fi ashirin,saboda kauyuka biyar ne suka shiga, akwai inda suka iske ana biki, suka yi ta harbin mutane, kuma ko da mutum ya ruga sai su bi shi su harbe shi. Sun bankawa rumbunar ajiyar kayan abinci da dama, sun kone su kurmus har da gidaje sama da dari biyu. Mutanen wadannan garuruwa duk sun tsere an kone garuruwan ba wanda ba’a sa wuta ba.

Majiyar ta kara da cewa ‘yan suntiri na garin Wurma da makwabta hadin gwiwa da jami’an tsaro sun bi su har dajin Safana, amma an ce ba’a gansu ba. Har sadda muke maganar nan da nike da kai ba’a gama tantance yawan barnar da suka yi ba na asarar rayuka da dukiyoyi.

Labarai Makamanta