Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Karkashe Mutane Da Ƙone Rumbunan Abinci

A ranar alhamis din da ta gabata ne, yan bindigar suka hari a garin Kabuke, da ke gundumar Runka da ke karamar hukumar Safana ta jihar Katsina, inda suka kashe mutane goma sha daya, da cinnama rubunan hatsi wuta.

Majiyarmu ta shaida mana cewa yan bindigar sun kwashe sama da awa ukku suna ta’addanci a garin, kuma mafi yawancin wadanda suka kashe ‘yan banga ne wadanda suka kawo wa garin dauki ne, sun kashe har mutum goma sha daya, wadanda makwabtan garin Kabuke ne.

A garin Jarkuka sun kashe mutum daya da garin Mai Jaura, an kashe masu mutum biyar da Daulai Mutum daya da garin Kwanar Dutse, sun kashe mutum biyu sai kauyen Kabuke sun kashe mutum biyu da kone rambunan abinci akalla hamsin na garin.

Harkar tsaro na cigaba da fuskantar kalubale a yankin Arewa maso yammacin Najeriya musanman a Jihohin Katsina da Zamfara, inda a kusan kullum Fulani ‘yan bindiga ke kai hare hare akan jama’a suna musu kisan gilla.

Labarai Makamanta