Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Daidai Lokacin Da Buratai Ke Kaddamar Da Atisayen Soji

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Yar Gamji mai nisan kilomita 150 daga karamar hukumar Batsari tare da kashe manoma 30 da ke aiki a gonakinsu, a daidai lokacin da Buratai ke ƙaddamar da atisayen dakarun soji.

‘Yan bindigar, kimanin su 200, sun dira kauyen a kan babura da misalin karfe 10:30 na safiyar ranar Litinin.

Mazauna kauyen sun sanar da jami’an tsaro halin da ake ciki kuma an turo dakarun soji domin bayar da gajin gaggawa.

‘Yan bindigar sun gudu zuwa cikin dazukan da suka fito bayan sun dan fafata musayar wuta da jami’an tsaro.

Jaridar Daily Trus ta rawaito cewa ya zuwa wannan mako da mu ke ciki, akwai mutane 6,914 a sasanin ‘yan gudun hijira guda uku da ke Faskari, Dandume da Batsari.

Yawaitar hare – haren ‘yan bindiga a yankin arewa maso yamma ya tilastawa jama’a da dama guduwa zuwa kasar Nijar.

A ranar mun kawo rahoton cewa rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta sanar da cewa ta kashe dumbin mayakan kungiyar Boko Haram.

A kashe mayakan ne yayin wani luguden wuta da jiragen yaki na rundunar NAF suka yi a sansanin mayakan da ke Parisu da Bula Bello a dajin Sambisa da ke jihar Borno.

Manjo Janar John Enenche, shugaban sashen yada labaran atisayen rundunar soji, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar da safiyar ranar Litinin.

A cewar Janar Enenche, rundunar soji ta kai harin ne; “ranar 3 ga watan Yuli a cigaba da atisayen rundunar soji na karasa murkushe mayakan kungiyar Boko Haram bayan samun bayanan sirri a kan wasu sansani da mayakan ke buya.

“Rundunar soji ta aika jiragenta na yaki bayan tabbatar da cewa mayakan suna buya a sansani. Jiragen sun yi luguden wuta, sun saki bamabamai da makamai ma su linzami a sansanin.

“Dumbin mayakan kungiyar sun mutu, sannan an lalata sansaninsu yayin ruwan wutar da jiragen suka yi,” a cewar wani bangare na jawabin.

Labarai Makamanta