A daren jiya Laraba wasu ‘yan bindiga da barayin shanu sun shiga ciki garin Batsarin Alhaji inda suka yi ta harbe-harbe, wanda har suka yi sanadiyar kashe limanin Jumu’a na garin mai suna Malam Tukur.
Sai dai zuwa yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ba ta fitar da wani rahoto dangane da faruwar lamarin ba.
Karamar hukumar Batsari dai ta jima tana fama da matsalar ‘yan ta’adda da suke yawan kai hare-haren ta’addanci.
You must log in to post a comment.