Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Bindige Babban Limamin Juma’a

Labarin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar wasu tsagerun ‘yan bindiga sun hallaka Babban Limamin Masallacin Juma’a na Sabon Garin Bilbis dake jihar bayan kin yarda su yi awon gaba da shi cikin gonarshi.

Limamin mai suna Malam Adamu Muhammad ya gamu da ajalinsa da safiyar Litinin a gonarsa dake wajen garin Faskari, sakamakon harbin Bindiga.

Garin Bilbis, wani gari ne dake karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, kuma mai iyaka da jihar Zamfara.

Wani ɗan kwamitin Masallacin Malam Lawal Mamman, wanda ya sanar da mutuwar Limamin ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun kwashe yara mata dake aiki tare da Malamin lokacin da suka kai harin.

A cewarsa, yan bindigan sun umurci Limamin ya bi su kan babur amma yace ba zai yi ba. “Sun fara yi masa barazana da bindiga amma yace babu inda za shi duk da cewa sun ce zasu kashe shi.” “Ya fada musu cewa yana da matsala a kafa kuma ba zai iya binsu cikin daji ba.”

“Bayan takaddamar ne, daya daga cikin yan bindigan yace kawai su kashe shi su bar wajen. Haka kuma suka kashe shi suka tafi da matan.

Labarai Makamanta