Katsina: Ruwa Ya Ci Matasa Uku

Da marecen ranar Alhamis ne, wasu matasa su uku ruwan wani tafki dake garin Tsagero a karamar hukumar Rimi a jihar Katsina ya yi sanadiyyar rasuwarsu.

Wani mazaunin garin Tsagero ne, ya shaidawa wakilinmu ta waya, inda ya ce wani daga cikin su ne ya je wanka a tafkin inda sauran biyu suka shiga neman shi, inda sai dai aka fiddo gawarwakin su, sun rasu.

Wadanda suka rasu akwai Amadu Alle Tsagero mai shekara ashirin da biyu da Saifullahi Mani, Mai shekara ashirin da uku da kuma Rabi’u Lawal Dankande, mai shekara talatin.

An kwashe tsawon awa biyu ana neman su a cikin Ruwa, tare da taimakon jami’an ba da taimakon gaggawa daga Rimi da kuma Katsina.

An yi jana’izar su da marecen jiya, kamar yadda addinin musulunci ya tanada. Allah ya jikan su da rahama.

Labarai Makamanta