Katsina: Mun Shawo Kan Matsalar Tsaro – Buratai

Yau Litinin Shugaban sojojin Nijeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya yi ganawar sirri da Maigirma shugaban kasa Baba Buhari Maigaskiya inda ya masa bayani akan tsaron yankin Arewa maso yamma.

Bayan kammala ganawar sirrin, ‘yan jaridu sun yi hira da Shugaban sojoji inda ya ce “mun shawo kan matsalar tsaron yankin, kuma mun samu gagarumar nasara karkashin Operation Hadarin Daji”. Sai dai yace akwai sauran matsaloli da ake fuskanta amma za a magance su ba da dadewa ba.

Wannan jawabin da shugaban sojojin ya yi a yau, ya zo ne kwana biyu da ‘yan bindiga suka yi wa sojojin sa harin kwanton bauna a garin Jibia jihar Katsina, harin da ya lakume rayukan sojoji kusan 30 a cewar wasu jaridu.

Jama’a shin kuna ganin ya dace shugaba Buhari Maigaskiya ya takaita ga karban rahoto ta hannun wakilansa kadai? Ko kuwa kuna ganin ya dace ace shugaban ya mallaki wata hanyar samun rahoton sirrin tsaro daga ‘yan leken asirinsa bayan rahoton wakilansa?

Ya kamata a tunatar da shugaba Buhari a ba shi wannan shawara cewa ya kara bude wata hanyar sanin bayanan sirrin tsaro daga yankunan Arewa maso gabas da Arewa maso yamma, domin ya dauki mataki talakawa su daina kuka.

Allah Ka ba mu mafita na alheri.

Labarai Makamanta