Katsina: Matashi Ya Hallaka Ɗan Sanda Da Al-Makashi

An gurfanar da wani matashi mai suna Yusuf Lawal, dan shekaru 22, a gaban babbar kotun Majestare ta Katsina, bisa zarginsa da hallaka kofurar din dan sanda mai suna Musa Isiyaku har lahira da almakashi, a yayin da dan sandan ya je kamo shi.

Kofurar Musa Isyaku mai shekaru 30, dan sanda ne dake aiki a carji ofis din yan sanda na cikin garin Malunfashi, ya gamu da ajalin nasa a ranar 5, 2019, a No 22 Layin Yanbori kwatas cikin garin Malumfashi,

Majiyarmu ta Punch ta rawaito cewa Yusuf Lawal ya caka wa dan sandan almakashin a cikinsa da a awazunsu, wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwarsa.

Lamarin ya afku da wajen misalin karfe goma da rabi na ranar, a lokacin da yan sanda suka kai samamen a unguwar bayan sun sami rahoton yan iskan gari sun addabi mutanen unguwar.

Bayan sauraren jawabin dan sanda mai gabatar da kara ASP Sani Ado, a yanzun haka kotun na cazar Yusuf Lawal da laifin kisan kai, a inda mai Shari’a Hajiya Fadile Dikko, ta dage ci gaba da sauran shari’ar har sai zuwa ranar 30 ga watan Janairun 2020

Related posts