Katsina: Masari Ya Sanya Ranar Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomi


Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Katsina, Malam Ibrahim Bako, ya bayyana a ranar Talata cewa za a gudanar da zaben kananan hukumomin jihar a ranar Litinin 11 ga watan Afrilu, 2022.

Bako ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Katsina.

Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a ranar Talata ne aka fara gudanar da gangamin yakin neman zaben.

Bako ya ci gaba da cewa, “Za a gudanar da zaben kananan hukumomin jihar Katsina a ranar Litinin 11 ga watan Afrilu, 2022, yayin da aka fara gangamin yakin meman zaben a ranar Talata 11 ga watan Janairu, 2022. Don haka idan aka yi lissafin daga yau har zuwa 11 ga watan Afrilu, 2022.zai kasance daidai kwanaki 90 da ake bukata don sanarwar zaben.

“Duk wani gangamin siyasa da yakin neman zabe za a fara ne daga ranar 11 ga watan Janairu kuma za a kare shi sa’o’i 24 kafin ranar gudanar da zabe.

Sannan yace “Za a gudanar da yakin neman zabe da gangamin siyasa bisa ka’idojin gudanar da zaben kananan hukumomin jihar da babu cikas.”

Bako ya jaddada cewa ‘yan takarar da jam’iyyun siyasa masu rijista ne kawai za a ba su damar shiga cikin zaben.

Labarai Makamanta