Katsina: Masari Ya Bada Umarnin Karantar Da Dalibai Da Hausa

Labarin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar Gwamna Aminu Masari ya umarci malamai a cibiyoyi daban-daban na ilimi a jihar da su fara koyar da yara da harshen Hausa.

Masari ya bayar da wannan umarni ne a lokacin kaddamar da wasu litattafai uku da suka shafi wakoki da adabi a kasar Hausa da kuma fassarar kamus na Turanci zuwa harshen Hausa wanda Mande Muhammad ya rubuta.

Gwamnan wanda kwamishinan ilimi, Farfesa Badamasi Charanchi ya wakilta, ya bayyana cewa irin wannan tsarin na koyarwa zai taimaka wa yara wajen inganta ilminsu.

Ya bayyana cewa an tsara manufofin kasa kan ilimi ne domin koyar da yara daga tushe cikin harsunan gida. Masari ya yabawa marubucin kan rubuta litattafai cikin harshen Hausa, inda ya bayyana yunkurin a matsayin wani shiri abin yabawa kuma mai kawo ci gaba a cikin al’umma.

Labarai Makamanta