Katsina: Malamin Makaranta Ya Kashe Daliba Da Duka

Ana zargin wani malamin lissafi na makarantar sakandare ta koyon Larabci (Government Girls Arabic Secondary School) dake cikin garin Fago a karamaar hukumar Sandamu ta jihar Katsina da yi wa wata dalibar duka wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dalibar mai suna Fatima Tasi’u.

Malamin da ake zargi da yin duka, mai suna Abubakar Suleiman, da ake wa lakabi da Sikiti, kamar yadda wasu suke fadi cewa asalinsa ba cikakken malamin makarantar bane, principal din makarantar ne ya dakko shi sojan haya kuma yana biyansa N5,000 duk wata.

A lokacin da yake bayyana yadda lamarin ya faru ga wakilin Daily Trust, mahaifin marigayiyar Malam Tasi’u Maikano dake unguwar Kofar Bai, ya ce a ranar 13 ga watan February ne mataimakin shugaban makarantar ya kira shi a waya yake ce masa ya shigo makarantar yarsa ba ta da cikakken lafiya.

Daga zuwan sa ne ake bayyana masu cewa, ‘yarsa ana zargin iskokai ne suka shige jikin ta, sakamakon ta fito wanka daga bandaki ta fadi ba lafiya, kamar yadda malaman makarantar suka sheda masa.

Daga bisani dai malam tasi’u maikano ya dauki ‘yarsa zuwa babban asibitin Daura, isar su ke dawuya likitan asibitin ya tabbatar masu da cewa ta rasu.

Mahaifin dalibar ya kara da cewa bayan kwanaki hudu da rasuwar ‘yarsa, sai ya je makarantar ya nemi da a bashi jakar ta da litattafan marigayiyar, inda a nan ne ya ci karo da wani rubutun da ta yi na ban tausayi mai ishara da abin da ya yi sanadiyyar mutuwar ta.

Dalibar ta rubuta a cikin wani dan litattafi da dalibai ke rubuta abin da ya shafi rayuwarsu a lokacin zamansu a makaranta wadda ake kira da ‘Diary’.

A cikin littafin mariganya Fatima ta rubuta cewa “Allah Sarki ranar Alhamis mun zo firef, sai Malam Habu Sikitu, ya doke mu har ya fasa mini goshi, kuma a lokacin banda lafiya ina wani irin zazzabi da ciwon baya a lokacin kamar na mutu nakeji” abin da marigayiyar Fatima ta rubuta kenan a cikin litattafinta kafin Allah Ya yi mata rasuwa.

Related posts