Katsina: Jami’an Tsaro Sun Tarwarsa Sansanin ‘Yan Bindiga

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar tawagar hadin gwiwa da ta kunshi rundunar yan sandan Najeriya da yan bijilante a karamar hukumar Safana ta Jihar sun kashe yan ta’adda biyu yayin musayar wuta a kauyen Sabon Dawa.

A cewar kakakin yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, wanda ya tabbatar da lamarin a ranar Laraba, ya ce an yi musayar wutan ne a yammacin ranar Talata, tsakanin ‘yan ta’addan da jami’an tsaro.

“A ranar 21 ga watan Yunin 2021 misalin karfe 5 na yamma, an samu kiran neman dauki cewa yan ta’adda masu yawa, dauke da AK-47 sun kai hari kauyen Sabon Dawa, Yankin Zakka, Karamar Hukumar Safana a Jihar Katsina. “

DPO na Safana ya jagoranci tawagar yan sanda da bijilante a yankin, suka yi musayar wuta da yan ta’addan, suka kashe biyu cikinsu sannan suka dakile harin da suka yi nufin kai wa.”

Kwamishinan yan sandan Jihar Katsina, Idrisu Dauda, a martaninsa, ya yabawa tawagar jami’an tsaron da mutanen garin saboda juriyarsu da cewa ‘sun daure sun kare garinsu daga harin yan ta’addan.’

Ya bada tabbacin cewa rundunar yan sanda za ta cigaba da yin duk mai yiwuwa don tabbatar da tsaro a garurunsu’.

Dauda ya bukaci mazauna garin su kira yan sandan a wadannan lambobin 08156977777 da 09053872247 don kai rahoton wani mutum ko mutane da ba su gamsu da su ba.

Labarai Makamanta