Katsina: Hukumar Kwastam Ta Yi Babban Kamu

Labarin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar Hukumar hana fasa-kwauri ta ƙasa Kwastam ta sanar da manema labarai cewa ma’aikatanta sun kama kayan da aka yi sumogal dinsu, kuma masu kayan sun biya Naira miliyan 38 cikin wannan watan da ake ciki.

Babban jami’in da ke kula da ofishin hukumar a Jihar Katsina, Dalhatu Chidi-Wada ne ya sanar da haka yayin wata ganawa da yayi da manema labarai a Katsina.

An ruwaito cewa bude kan iyakar Najeriya da Nijar a garin Jibiya ya taimaka wa yawancin al’umomin yankin su gudanar da harkokin kasuwancinsu kamar yadda doka ta tanadar.

Dalhatu Chidi-Wada ya ce yawan kayan da ake shigarwa da fitarwa kan iyakar ta Jibiya cikin watan da ya gabata ya hada da tan 4,000 na nau’in gas na LNG da tan 1,000 na siminti.

Labarai Makamanta