Katsina: Hatsarin Babur Ya Ci Ran Ɗan Gidan Mangal

Allah ya yi wa ɗan Shahararren ɗan Kasuwar nan kuma mai Kamfanin Jiragen Sama Na Max Air dake birnin Katsina, Alhaji Ɗahiru Barau Mangal, wato Nura Dahiru Mangal rasuwa Sanadiyyar hatsarin da Mashin ɗin nan mai gudu na tsere watau (Bike).

Alhaji Nura Dahiru Mangal ya yi hatsarin da misalin ƙarfe 4:00 na Yammacin yau Laraba kusa da Kwalejin Hassan Usman Katsina.

Majiyarmu ta shaida mana cewa za’a yi jana’izarsa gobe Alhamis da Misalin Karfe 10:00 Na Safiyar Gobe A Masallacin Alhaji Dahiru Bara’u Mangal, Dake Kofar Kwaya, Katsina.

Mashin ɗin Bike na da matuƙar gudu sosai hakan ya sanya yake da hatsari, kuma mafi yawan ‘ya’yan masu hannu da shuni na sha’awar hawan sa, idan jama’a za su iya tunawa irin wannan Mashin ɗin ne Yusuf Buhari ɗan gidan Shugaban ƙasa ya taɓa hatsari da shi a shekarar bara.

Labarai Makamanta