Katsina: Har Yanzu Ban Yanke Shawarar Tsayawa Takarar Gwamna Ba – Sanata Yar’adua

Rahotanni daga birnin Katsina na bayyana cewar Sanata Abubakar Sadiq Yar’adua ya ce har yanzu yana tuntubar magoya bayansa da masu ruwa da tsaki kuma zai bayyana matsayinsa a nan gaba, gabanin zaben gwamna na 2023 a jihar Katsina.

Yar’adua ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 19 ga wata Yuli, lokacin da ya karbi bakuncin wakilan magoya bayansa daga dukkanin kananan hukumomi 34 na jihar ta Katsina.

Abubakar Yar’adua ya ce yana kan neman shawarwari kafin ya yanke hukuncin neman takarar kujerar gwamnan Jihar a babban zabe dake tafe na shekarar 2023.

“Ina ta samu kiraye-kiraye daga dukkan sassan jihar, suna tambayata game da burin zama na gwamna kuma ina fada wa mutanena cewa har yanzu muna ci gaba da tuntubar shugabannin jam’iyyarmu a kan wannan batun kuma zan sanar da matsayina idan lokaci ya yi.”

“Ina da yakinin cewa ba ‘yan siyasa kadai ba har ma da dukkan ‘yan jihar za su yi maraba da wannan tunanin wanda ba za a bar wani rukuni ya karkatar da jam’iyya ba ko kuma ya tursasa dan takara ba.

Wannan shi ne abin da ake fata ga shugaba nagari wanda zai saurari dukkan bangarori kuma ya yi adalci ga duk wanda abin ya shafa.” Ya yi gargadin cewa idan har wata kungiya ko wani bangare na ‘yan siyasa a jihar suka yi kokarin rusa kyakyawan tsari da gwamnan ya yi, jam’iyyar za ta gamu da rarrabuwar kai a jihar.

Labarai Makamanta