Dan Takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya shiga jihar Katsina cikin nasara yayin da ya isa jihar da ayarin yakin neman zaben sa a ci gaba da rangadin tuntuba da yakin neman zaben shugaban kasa.
Da yake jawabi a yayin gangamin wanda ya tara dubban jama’a, ciki harda kwamitin gudanarwa na Jam’iyyar na kasa da mambobin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Atiku ya jaddada alkawarin da ya yi na Samar da tsaro tare da sake bude iyakokin kasar nan na kan tudu domin saukaka harkokin Zirga-Zirga da kasuwanci domin zaman lafiya.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya shedawa mutanen jihar ta katsina cewar a shirye yake ya aiwatar da manufofin dake cikin kundin tsare-tsaren sa, wanda ya yi wa lakabi da ALKAWARINA DA YAN NAJERIYA idan aka zabe shi. Wazirin Adamawa ya bukaci jama’ar jihar da dukkan Yan Najeriya su zabi Jam’iyyar PDP, inda yace gwamnatin PDP wadda aka Yi da shi ta Fi gwamnatin yanzu wadda ta jefa mutane a mawuyacin hali.
Da yake nasa jawabin, shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Dr Iyorchia Ayu yayin da yake Karbar Alhaji Mustapha Inuwa tsohon sakataren gwamnatin katsina har karo biyu tare da wasu dubban yayan Jam’iyyar APC da suka dawo PDP, ya yi kira ga mutanen jihar ta katsina su zabi Atiku da sauran Yan takarar PDP a zaben dake tafe. Shima Alhaji Inuwa ya tunawa mutanen Katsina game da Mulkin Yar’adu’a a jihar.
Sauran manyan baki da suka yi jawabi a taron sun bayyana yakinin cewar PDP zata lashe zaben shekarar 2023 kuma Jam’iyyar ta shirya karbe jihar katsina Daga APC. Daraktan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP Aminu Tambuwal yayin da yake wa dandanzon mutanen jawabi a harshen Hausa ya bukace su dasu zabi PDP domin dorawa kan ayyukan alheri na marigayi Umaru Musa Yar’adu’a.
A nasa bangaaren, gwaman jihar Delta kuma Dan Takarar mataimakin shugaban kasa na PDP Dr Ifeanyi Okowa ya jinjinawa Atiku Abubakar, inda yace shugaba ne da za a iya amince masa ya jagoranci kasar nan domin fitar da Ita daga matsalolin siyasa dana tattalin arziki da APC ta jefa kasar a ciki.
Shima a nasa jawabin, shugaban kwamitin yakin neman zaben na shugaban kasa na PDP gwamnan jihar Akwa Ibom Udom Emmanuel ya godewa dandanzon magoya bayan Jam’iyyar da suka cika filin wasa na Muhammadu Dikko Kakanda.
Sannan ya yi kira ga al’ummar jihar su zabi PDP domin tsaron kasa da alkinta dukiyar kasa.
Abdulrasheed Shehu
Mataimaki na Musamman ga Mai girma Atiku Abubakar kan kafafen yada labarai.
20 ga Disamba 2022.
You must log in to post a comment.