Katsina: Buhari Ya Ziyarci ‘Yan Gudun Hijira

Shugaba Muhammadu Buhari ya Ziyarci sansanin ‘yan gudun Hijira dake karamar hukumar Batsari ta Jihar Katsina.

Karamar hukumar Batsari na daya daga cikin kananan hukumomin da Ke fuskantar barazanar tsaro a Jihar katsina.

Gwamna Aminu Bello Masari ne ya tarbi tawagar shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau laraba inda Gwamnan yayi godiya ga gwamnatin tarayya bisa karin jami’an tsoron da aka Karo yankin wanda hakan ya takaita ayyukan ta’addanci a yankin da sassan Jihar katsina.

Gwamna Masari ya kara da cewa ” duk da dai ba a rasa satar shanu, garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka nan da chan, Amma gwamnatin sa na iya bakin kokarin ta da sauran jami’an tsaro wurin shawo kan wannan matsalar musamman ta hanyar shirin sulhu da Kuma afuwa da ake yiwa tubabbun yan ta’addan.

Related posts