Katsina: An Yi Odar Karnuka Domin Gadin Makarantu

Gwamnatin jihar Katsina ta amince da tura Karnuka gadin makarantun kwanan jihar domin taimakawa jami’ar tsaro wajen dakile ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Kwamishinan ilimin jihar, Dr Badamasi Charanchi, ya bayyana cewa gwamnatin ta yanke shawaran haka ne domin karfafa matakan tsaro a makarantun kwanan jihar.

“An bamu shawaran tura Karnuka kowace makaranta saboda suna da horaswa na gano wani mai yunkurin kutse fiye da dan Adam.” “Wadannan karnukan idan aka tura su, zasu ankarar da dalibai da sauran jami’an tsaro idan wasu yan bindiga na kokarin zuwa.”

“Jami’an tsaro ne suke bada wannan shawara kuma mun yanke shawaran gaggauta amfani da shi saboda halin rashin tsaron da muke ciki.”

Labarai Makamanta