Katsina: An Tsige Hakimin Da Ke Harka Da ‘Yan Bindiga

Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar Majalisar sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ta tumɓuke rawanin hakimin ƙanƙara biyo bayan gano cewa yana da hannu dumu-dumu wajen taimaka wa yan bindiga.

Katsina Daily post ta wallafa a shafinta na facebook cewa masarautar ta gano sarkin Pauwan Katsina kuma hakimin ƙanƙara, Alhaji Yusuf Lawal yana taimaka wa wasu yan bindiga wajen gudanar da ayyukan ta’addacin su.

Bisa wannan dalilin ne majalisar sarki ta tsige shi daga muƙaminsa na Sarkin Pauwa hakimin kankara kwata-kwata.

A kwanakin baya majalisar sarkin ta dakatar da hakimin bisa zarginsa da hannu wajen taimaka wa yan bindigan dake kai hare-hare a faɗin jihar ta Katsina.

A rahoton da katsina daily post ta ruwaito ya nuna cewa sakataren fadar mai martaba sarkin Katsina kuma sarkin yaƙin Katsina, Alhaji Bello Mamman Ifo, shine ya tabbatar da tsige hakimin.

Labarai Makamanta