Katsina: An Kama Dan Bindiga Mai Shekara 14

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar Rundunar ‘yan sandan Jihar ta ce ta kama wani yaro ɗan ƙasa da shekara 20 da zargin shiga ayyukan ‘yan fashin daji da suka addabin yankin arewa maso yammacin ƙasar.

A cewar kakakin ‘yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, yaron mai shekara 14 ya amsa laifin kashe mutum biyu yayin wani hari da suka taɓa kaiwa.

“Yaron yana cikin waɗanda suka kai hari a Mallamawa cikin Ƙaramar Hukumar Jibia da kuma wasu a wajen Jihar Katsina, inda ya ce ya tuna lokacin da ya kashe mutum biyu,” in ji SP Gambo.

“Kuma ya shiga hare-haren da aka kai a Dankulumbo da Kukar Babangida, duka a Jibia. Sannan ya yi ƙwacen shanu da ba a tantance adadinsu ba.”

Ba kasafai ake kama yara ƙanana ba da zargin taimaka wa ‘yan fashin duk da cewa ‘yan sanda sun sha kama mata da kayayyaki a kan hanyarsu ta kai wa miyagun.

Har yanzu wasu sassa na jihohin Kaduna da Zamfara da Katsina da Neja – inda ‘yan fashin suka fi addaba da kashe-kashe da satar mutane – na cikin ɗaukewar layukan sadarwa, matakin da gwamnatoci suka ɗauka da zummar daƙile ayyukan maharan

Labarai Makamanta